AREWA KO DAI YAUDARA

 

2010

Arewa! Da zarar ka ji wannan kalma to ka sani fa cewa ‘yan boko da masu mulki na son amfani da ita don ci gaba da danniyar da su ke wa talakawan arewa. Wannan kalma ta samo asali tun kafin turawa su hade kudancin da arewacin Nigeria a 1914. Sahun farko na ‘yan arewa da suka yi fafutukar kare hakkin wannan yanki, irinsu Malam Aminu Kano, Sardauna, Tafawa Balewa, Ribadu da sauransu, sun bar duniya ba tare da sun mallaki wani abin azo a gani ba. Wasunsu ma saboda arewan aka kashe su.

Kaucewar su ke da wuya mabiyansu sun yi kokarin kamantawa wajen kamewa daga cin dukiyar jama’a, kuma an tabbatar ba su yi sata ba, irinsu shugaban kasa Gen. Gowon da Murtala. Abin takaici, su kuma su na kaucewa sai aka sami shugabancin Obasanjo da Yar Adua, wadanda daga lokacin su ne aka fara samun shugabanni suna tara kazamar dukiya kuma an halatta cin hanci da rashawa cikin al’amuran gwamnati. An kafa kamfanin karfe na Ajaokuta wanda bayan tsawon shekaru da lakume sama da Naira Biliyan 960 bai samar da karfe ko guda ba. Yawa-yawan wadannan kudade ne aka sace aka dinga siyan kadarori a waje da gida. Wato an sami sahun farko na mahakunta masu kazamin arziki. Wannan ya baiwa ‘yan siyasa damar watanda da arzikin kasa, daga 1979-1983 inda aka rasa sama da naira Tiriliyan biyu, sannan bashin kasashen waje a karon farko ya kai sama da naira Tiriliyan daya, kuma tattalin arziki ya fadi da kashi 8 kafin soja su karbe gwamnati..

Sardauna ya assasa kishin arewa kuma ya yi aiki tukuru wajen habaka ta, amma sai mabiyansa suka zama mara sa da’a da kishi. Da zarar ka ji sun busa begilar arewaci to, ka tabbata an taba su ko kuma suna fuskantar barazana. Sanin kowa ne cewa ‘yan arewa su ne suka fi kowa darewa kujerar mulkin kasar nan, idan ka cire Murtala da Buhari (wadanda aka kifar daga gwamnati) za mu fahimci cewa ‘yan arewa su ne su ka kashe kasar nan, musamman ma arewacin da suke tunkaho. Yan arewa su ne su ke hada kai da abokansu na kudancin kasar nan da kuma na kasashen wajen karya kasar.

Wannan ya kawo mu cikin halin da ake ciki a yau, na cewa PDP na neman fitar da mutum guda daga arewa wanda zai kalubalanci Goodluck a zaben badi. Kafin mu je ga su ‘yan takara, idan mu ka duba mutum 17 da ake kira dattijan arewa da ke cikin wannan kwamiti kafin a rage su zuwa tara, ina tabbatar maka da cewa yawancinsu dashen Sardauna ne, kuma zan rantse babu wanda ba Gwamnati ce ta tallafi karatunsa har ya gama ba. Akasarinsu sun ba shekaru sittin baya amma duk wanda a yau ka ce ya zo ya rike ofishin Minista da gudu zai karba duk da cewa sun fi shekaru arbain su na ayyuki iri-iri. Mu tambayi kan mu, shin akwai lokacin da wadannan dattawa su ka taba zama suka kuma jajirce ganin cewa sun samo wa ‘yan arewa mafita akan babban bala’in da ke damun mu na almajiranci? Sanin kowa ne akwai almajirai ko’ina a duniya (don ko a Ingila na ba almajirai sadaka) amma babu inda ake yinsa kamar arewacin Nigeria. Malamai, Sarakai, Gwamnatoci da su Dattawan arewa sun halarta barace-barace don sun kyale ta ba tare da samo wa miliyon yara mafita ba. Duk da cewa wadannan dattawa sun yi karatu a bagas, da a ce wani makwabcinsu zai kai kuka cewa ga dansa ya na bara a biya masa kudin makaranta, da ya sha mamaki. Wadannan mutane za su iya samar wa da arewa mafita kuwa?

Jajircewarwar wadannan dattawa wajen fitar da Atiku tsakanin masu takara, ba wani abu ba ne sai kare muradunsu, kuma dalilin da ya sa su ka zabi Atiku ba don komai ba ne sai don sanin cewa a yanzu babu wani dan takara da ya fishi kudi. Don haka a nasu lissafin shi ne zai iya kashe biliyoyin da ake sa ran kashewa don tunkarar takarar fitar da gwani na PDP.

Idan muka dawo kan ‘yan takarar, misali shi Atikun da aka zaba, me ya ke da shi wanda zai nuna wa Nigeria ko arewacin da ya yi don habaka kasa ko yankinsa? Titunan arewacin Nigeria duk sun mutu a lokacin da yake gwamnati, kuma titin da ya tashi daga Gombe zuwa jiharsa shine mafi muni a lokacinsa. Akwai kwangila da aka ce an so a yi, ta kare gusowar Hamada da za ta zama wata kariya daga Gabashin Borno ta dire har arewacin Sokoto, amma saboda burika irin na siyasa bai sami damar tabbatar da aikin ba har ya bar gwamnati. Ko da yake dai ya yi gagarumar rawa wajen kafa ABTI amma sai dai kash, yaranmu almajirai da sauran ‘yayan talakawa ba za su iya biyan kudin shiga ba. Amma duk irin zagin da ake wa Obasanjo, a lokacin mulkinsa karo na biyu ya habaka tattalin arzikin kudu maso yamma. Domin duk wani abin da ake sana’antawa a Nigeria (kama daga man goge baki zuwa biskit) sama da kashi 80% daga Ibadan-Abeokuta-Lagos ake sarrafa shi, sakamakon karfafa masana’antunsu da ya yi. Amma a lokacin da yake da murya da iko kan gwamnonin arewa, wane abu ya saka gwamnonin su ka yi don habaka NNDC? A lokacinsa sama da rabin masana’antu arewa su ka mutu, duk wata masana’anta ta sutura a Kaduna da Kano babu su a yau.

Babangida kuwa, ya zama ba ka jin duriyar sa a wannan kasa sai fa idan rurumar Gwamnati ta taso. Ya na sauka a 1993 babu wanda ya sake jinsa, har sai bayan kashe Abacha, nan  da nan sai ga shi a sahun gaba wajen dora Abdussalam. Da kuma aka hura begilar siyasa sai ya je ya jajubo Obasanjo da tunanin idan ya kammala wa’adinsa za’a rama wa kura aniyarta. Amma sai tsohon na Ota ya murza gashin baki ya kuma dafa IBB da guminsa, yadda shi da kansa ya janye. Ba mu sake jin duriyarsa ba sai bayan mutuwar ‘yar Adua shine ya dawo da takararsa. A zamanin Babangida me ya yi wa kasar?sanin kowa a zamaninsa, matsalolin kasar nan su ka cakude musamman rashawa da cin hanci kuma bai taba fitar da wani yunkuri na yaki da su ba. A karon farko an zargi jami’ai da hada hadar kwayoyi a mulkinsa. Dattawan arewa sun san cewa ya na da matsala da kudancin kasar nan saboda June 12, ina zaton hakan da kuma kasancewar yanzu babu kudi a hannunsa kamar da, shi ya sa su ka yi watsi da shi. A cikin wadannan dattawa da su ka yi zabe, M.D Yusuf ya taba gaya wa Karl Maier (Shahararren Dan Jarida Bajamushe wanda ya rubuta “The House has Fallen” game da Nigeria) cewa “Ai gara Abacha da Babangida saboda shi Babangida ai babu abinda yayi banda habaka rashawa da lalata al’umma, amma shi Abacha  ya saka mutane cikin tsoro ne kawai, Abacha na mutuwa aka fita daga tsoron; amma lalacewar al’umma na nan kuma tana cin jikin alumma”. Kuma Babangidan nan ne lokacin da Magaret Thatcher ta ba shi shawara cewa ya rikide daga soja zuwa farar hula, da bakinsa ya ke cewa bai jin zai iya aiki a matsayin farar hula saboda “Na saba in bada oda a dauka, yaushe zan koma ina zawarci ko roko (kafin na aiwatar)” Amma sai ga shi a yau ya dawo yana nema. Da gangan ya hada rikicin June 12 saboda da bakinsa ya ce “Ba wani Mahaluki, daga kasar yarbawa ko da abokansa (Abiola) da su ka bashi kudin kanfen kamar ni” sannan an yi zaben da ba’a taba irinsa ba a kasar domin kusan kowa ya yaba (gida da waje). Amma Babangida ya soke, da aka matsa masa sai ya hakura ya sauka tare da barin Abacha a baya saboda kamar yadda ya fada a hirarsa da Karl Maier “A wannan lokaci na san cewa da zarar na bar office, (wato shi Abacha) zai hanbare gwamnatin (Abiola)”.  Sannan shi ko Babangida ko irin ‘yar makarantar Atikun bai yi ba, af! ashe matar sa ta yi sakandaren ‘yayan masu hannu da shuni. A karshe zan rufe zancen Babangida da kalamansa inda ya ke cewa game da Nigeria “Wani lokaci sai kaga kamar sama da kasa zata hade, amma duk tsanani, duk turka-turka, sai an sami mafita”. Kuma wannan Magana ta Babangida gaskiya ce saboda talakan Nigeria bai san kansa ba.

Idan muka matsa kan Ali Gusau kuwa, ba sai na ce komai ba saboda dattawan arewan da kansu sun yi cikakken bayani na kasancewar babu wani cikinsu da ya jefa masa kuri’a. Shi kuwa Bukola idan ka duba mutane biyun da suka ba shi kuri’arsu zaka tabbatar da maganar marigayi Malam Aminu Kano da ke cewa “Nigeria ta kowa ce amma kowa ya san gidan ubansa”

To idan muka koma kan Uban gayyar a PDP, wato Goodluck zamu fahimci cewa tamkar ci gaba ne na gwamnatin Obasanjo. Obasanjo cikin hikima ya zaizaiye dattijan kasar nan daga cikin mahimman al’amura na mulki sai dai kuma ya kawo bara gurbin matasa a maimakon su. Yawancin su ‘yan boko ne masu digiri ko digirgir (Inda a ka sami Yar Adua da Goodluck masu digiri). Face ‘yan kalilan cikin matasan, yawancin su babu kasar ko ‘yayanta a zuciyar su. Abinda kowanne dan Nigeria zai tambayi kansa game da takarar Jonathan shine, me ya yi tun sanda ya hau mulki zuwa yau, wanda zai ja hankalin ‘yan kasa su yarda cewa idan aka bashi dama zai gyara kasar?... idan ka gama tunaninka kaf sai ka ga babu wani abin a zo a gani banda matsaloli da ya kawo. E, matsaloli mana, ya ya shugaban kasa zai sa kafa ya shure yarjejiniyar jam’iyyarsa ta karba-karba (duk da cewa dai ba dumokuradiya ba ce). Sannan da aka dasa bom ranar yancin kai, ya yi farat kafin a yi bincike ya zargi abokan adawarsa na arewa. Wallahi idan kasar masu hankali ce da tuni ya sauka daga mulki. Kuma abu mafi muni shine cewa Marigayi Yar Adua yayi kokarin da ba shugaban da ya yi nan kusa, domin a karo na farko yan fafutukar Niger-Delta sun yarda da ajiye makamai da yin sulhu. Cikin dan karamin lokaci, cikin shekaru goma, gangar mai kusan rabin miliyan da ke salwanta sakamankon fandarewar su ta dawo lalitar gwamnati. Amma ya na hawa yayi watsi da duk shirin sulhu, yadda kai tsaye ma suka dasa bom kusa da inda ya ke bikin cikar shekaru hamsin na ‘yancin kai. Wanda ya kasa kawo zaman lafiya ga yankinsa, ya ke kuma neman tunzura wutar kabilanci zai iya zama mutumin da zaka yarda a ba kasa? Mutumin da ya kasa, ko don yaudara, ya yi wasu ‘yan abubuwa da za su sa ace lallai yakamata a gwada shi.

To ina mafita a Nigeria? Wasu zasu yi caraf su ce Buhari amma ka da su manta cewa duk da Buhari mai gaskiya ne ba zai yi mulki shi kadai ba kuma mutanen da ke kewaye da shi babu abinda ya raba su da mutanen PDP sai dai kawai su ba a cikin mulki su ke ba. Alal hakika ba zamu taba samun canji ba a Nigeria har sai talakawa sun canza rayuwarsu, wato su koma masu bin doka da oda a tsakaninsu, a daina girmama ka don kana da kudi ko mulki sai don me ka yi na alheri a rayuwar mutane. Sannan su yi watsi da kabilanci na yare da addini. Da zarar talaka ya fara haka tabbas mutane mayaudara sun daina yaudararsu, kuma zaka ga cewa mutanen kirki ne kawai zasu rika zawarcin kuri’unsu domin mutumin banza ya san cewa talaka ba zai taba zabarsa ba. Amma kafin mutane su shirya yin wannan tsari, na juyin-juya-hali na halayya, sai su yi kokarin zaben da ake cewa “Da baki-kirin, gwamma baki-baki”.

Comments

Popular posts from this blog

MALAMAI SUN TAIMAKA WAJEN RUSA AREWA

JINNS: SPIRITUAL FANTASY OR SCIENTIFIC POSSIBILITY?

THE NORTHERN WAHALA!