LAIFIN RAHAMA SADAU, AFAKALLAH AND KANNYWOOD
Asalin Rahama Sadau yar rawar gala ce kafin Ali Nuhu ya
kyalla ido ya hango ta da fahimtar cewa wannan yarinya za ta iya zama wata
gagarumar jaruma. Kasancewar Alin ne ya kawo ta masana’antar hadi da cewa ta
iya acting, kafin ka ce me, ta fara samun shahara yadda ta dusashe sauran
taurari mata. Cikin abubuwan da su ka daga likkafar wannan yarinya aka san ta
sosai bai rasa nasaba da kutsa kanta cikin rigingimu iri-iri tun shigowarta
wannan masana’anta, watakila ta na ganin cewa ta hanyar saka kanta cikin
rikice-rikice su ne za su dawwamar da tauraronta a sama ba tare da la’akari da
irin al’ummar da ta sami kanta a ciki ba.
Rikicin baya bayan nan ba shi ne na farko, ko na biyu ko na
uku ko hudu ba, shine rikici na biyar da ta sami kanta idan zamu iya tunawa. A
farkon shigowarta masana’antar Kannywood ta sami rikici da babban jarumi Adam
Zango yayin da ta je wajen da ya ke daukar wani fim nasa kuma ta tashi aikin
tare da yin fashe-fashe, abinda ya kai su gurfana gaban kwamitin ladabtarwa na
MOPPAN inda a karshe ta bada hakuri da alkawarin ba za’a sake ba. Rahama ta
sake samun kanta cikin wani rikicin inda wani mai shirya fina-finai a Maiduguri
ya dauke ta a matsayin jaruma amma sakamakon sabani da su ka samu ta je ta
dauko masa sojoji wadanda su ka zo wajen daukar fim din su ka hargitsa shi
yadda aikin bai yiwu ba. Ance sakamakon bakin cikin wannan hasara da Rahama ta
jaza masa ya sa yayi hadari a hanyarsa ta dawowa inda ya mutu.
Ana nan sai gashi ta sake jajubo wata babbar rigimar wadda ta
dauki hankali mutane a fadin kasar inda ta yi wata waka da wani mawaki mai suna
ClassiQ inda ta ke rungumarsa. Wannan hoton bidiyo ya harzuka wasu mutane da ke
ganin cewa bai dace ba, yadda sakamakon korafe-korafe ya sa kungiyar MOPPAN ta bakin
Salisu Officer a jaridar Guardian in day a sanar da cewa “An kori Rahama gaba
daya daga masana’antar…sakamakon rashin da’ar da ta nuna a wata waka da ta ke
rungumar wani”. Kafin cimma wannan matsaya shugabannin na MOPPAN sun kai ruwa
rana tsakaninsu inda wasu ke ganin a dakatar da ita shekaru uku amma masu ra’ayin
a kore ta ya yi rinjaye inda mutane shida cikin goma su ka amince da korarta,
ganin cewa Rahama duk da alkawuran da ta sha dauka a baya bai hana ta kaucewa
rikice-rikice ba.
Ba dadewa da korarta ba sai ta
sami gayyatar shahararren mawakin Amurka, Akon, tare da hadin gwiwar mai shirya
fim na Nollywood Jeta Amata, zuwa cibiyar fina-finai ta duniya wato Hollywood.
Akon ya sanar a shafinsa na tiwita cewa “Ya kamata mu karfafa matan mu da azama
su zuwa ci gaba, karbarsu ya fi korarsu” a matsayin wani shagube ga hukumar
MOPPAN. Kungiyar MOPPAN ta mika wannan hukunci na korar Rahama ga babban
daraktan hukumar tace fina-finai ta Kano wato Afakallah, wanda ya saka hannun
amincewa. Bayan nan sai Rahama ta ci gaba da harkokinta a wajen Kano ganin
yadda likkafarta ta daukaka kuma ta ci gaba da yin harkokin fim nata na kanta
da kuma a masana’antar Nollywood. Bayan lokaci ya ja sai Rahama ta fara kokarin
yadda za ta dawo Kannywood a yafe mata kamar yadda wani jami’in MOPPAN ya
shaida min a Kano cewa ta yi kokarin baiwa wani jami’in MOPPAN cin hanci na
Naira dubu hamsin domin ya hada ganawarta da masu ruwa da tsaki a MOPPAN ko
Allah zai sa su yafe mata ta dawo cikin masana’antar, abinda ya ki yayi.
Katsam a makon da ya gabata
sai ga shi ta sake jawo wata babbar rigimar wadda ba ta taba yin irinta ba
sakamakon saka wasu hotuna na ta da ke nuna tsiraicin bayanta, abinda ya ja
wani wanda ba musulmi ya yi kalaman batanci ga Annabi Muhammadu. An ce Rahama
ba ta cire, ko maidawa mutumin martini ba har na tsawon sa’o’i sama da ashirin.
Kuma wasu cikin kawayenta sun yi kokarin hana ta saka wannan hotuna tun asali
sanin yadda za su iya kawo cece-kuce. Anan ya kamata mutane su sani cewa a duk
duniya, hatta a Amurka da kasashen yamma, akwai abinda ake ganin bai kamata a
yi shi a idon jama’a ba, wanda ya sa dokar kasashe ke da hukunci kan abubuwa na
bai dace ba. Irin wannan doka na daukar “Duk wani abu da ya jibanci yada wani
abu cikin jama’a da ya danganci batsa, zagi ko abu mara kyaun gani da zai iya
tada hankalin jama’a”. Wannan ya sa Kotun Kolin Amurka (kotun da ma ta halatta
auren jinsi) ta tabbatar da wannan doka wajen hana furta kalaman zagi/ashar a
duk wani shirin talabijin, musamman domin a kare yara masu tasowa. A shekarar
1984 lokacin da Madonna ta saki bidiyon wakarta “Like A Virgin” ta fuskanci
caccakar jama’a har daga fadar Fafaroma. Haka ma wakar Salt N Pepa a shekarar
1991 wadda ke maganar jima’i (Lets talk about sex) da kuma wakar TLC “Aint too
proud to be” da ire-iren wadannan wakokin duk sun fuskanci suka. Laifin Rahama
anan shine a matsayinta na musulma ta san cewa akwai ka’aidar shiga wadda
addini ya tanada a Qur’ani cewa dole mata su rufe wuraren da za su iya jan
hankalin maza musammam daga kafada zuwa kasan kwauri a duk sanda su ke a bainar
jama’a. Hikimar Qurani shine rufe wadannan wurare zai rage abubuwa irinsu fyade
da sauransu, kuma bude su na iya kawo hadurra da matsaloli, musamman idan muka
yi la’akari da cewa ganin bayanta a bude ya sa wani wanda ba musulmi ba ya yi
kalaman batanci ga Annabi Muhammadu. Da ba ta saka wannan hoto ba ka ga irin
wannan batanci da bai faru ba. A matsayin halin da Najeriya ke ciki na matsi da
fushin matasa, yadda kwanan nan mun ga yadda zanga-zangar Endsar ta haifar da
mummunar tarzoma, wannan kalamai nabatanci na iya rura wutar rikicin addini
wadda ba za ta haifarwa kowa da mai ido ba. Amma dai Babban Sufeton yan sanda
ya yi wuf ya umarci kwamishinan yan sanda na Kaduna ya gaggauta bincike.
Shi kuma Babban Daraktan
hukumar tace fina-finai, Afakallah, nasa laifin na da yawa, domin kasancewar
wanda MOPPAN ta tuntuba kuma ya sahale da korar Rahama tun asali, bai kamata ya
dawo shi kadai ba tare da tuntunbar MOPPAN din ba wajen yi mata afuwa yadda ya ce
hukumarsa za ta ci gaba da tace fina-finanta. Yin hakan ya karfafa Rahama wajen
ci gaba da yin abinda duk ta ga dama da kuma zaizaiye ikon wannan kungiya a kan
yayanta. Lokacin da aka sanar da baiwa Afakallah wannan mukami nasa, na yi
matukar farin ciki ganin cewa ya fito daga wannan masana’anta don haka na dauka
cewa zai kawo canji da aka dade ana tsammani a wannan masana’anta, amma daga
dukkan alamu ya kasa. Sanin kowa ne cewa gwamna Kwankwaso abokin masana’antar
Kannywood ne kuma ya karfafa ta ta hanyoyi da dama domin hatta ita wannan
hukuma da Afakallah ke jagoranta shi ya kafa ta. Amma a bayyane ya ke cewa ba
wani gwamna da ya jawo yan masana’antar cikin gwamnati irin gwamna Ganduje (duk
da cewa a daya hannun kuma ana yiwa gwamnatinsa kallon ta na yi wa wasu yan
masana’antar bita da kulli, idan mu ka duba yadda aka kama Naziru Sarkin waka
da Sunusi Oscar), domin akalla yan masana’antar da dama sun sami mukamai a
cikin gwamnatin. Bayan Afakallah, akwai Al-Kinana, Yahanasu Sani, Rashida
Adamu, Nura Hussein, Ado Baffa (Marigayi), Ali Lilo da Ibrahim Ibrahim.
Masana’antar Kannywood ba taba
samun irin wannan tagomashi ba kuma ya ci a ce wadannan jami’ai sun kawo wani
gagarumin canji ta hanyar samar da hadin kai da tallafi na gwamnati wajen ci
gaban masana’antar. Amma abin takaici kusan duk wadannan jami’ai bukatar
gabansu su ke yi domin ba wata hujja a kasa wadda ta nuna sun kawo wani
gagarumin canji. Shi kansa Afakallah wanda ke da mafi girman mukami cikinsu, a
bayyane ya ke ya gaza musamman idan aka yi la’akari da ikirarin da daya daga
cikin jagororin masana’antar, Hamisu Iyantama ya shaida min, cewa ya kasance
shugaban kwamitin farfado da kasuwanci a masana’antar wanda Afakalla ya kafa.
Cikin hira ta da shi ya tabbatar da cewa wannan kwamiti na su ya lalubo hanyoyi
ingantattu wajen farfado da kasuwancin masana’antar wanda ya durkushe, ta kokarin
farfado da sinimomi musamman marhaba, wanda abin bai dore ba. Kuma sun jawo
hankulan masu gidajen kallo wajen ganin sun saka nuna fina-finan hausa a cikin
jadawalinsu. Sannan ya kara da cewa sun yi kokarin yakar satar fasaha ta hanyar
zuwa jihohi da dama domin jawon hankulan masu rarraba fina-finai su daina
karbar kowanne fim sai da takardar shaidar hukumar tace fina-finai. Har ila yau
kwamitin ya hada taro da yan downloading a gaban jami’an tsaro domin nuna musu
illar satar fasaha. Haka nan sun yi kokarin samar da dandalin yanar gizo domin
tallata fina-finan masana’antar. Abin tambaya shine menene dalilin da wadannan
kyawawan shirye shirye ba su kai gaci ba? Iyantama ya dora laifin ga Afakallah
da cewa bai iya mu’amala da jama’a ba kuma tsawon watannin da su ka kwashe su na
wannan aiki hatta dan alawus na zaman aiki ko na tafiye-tafiye hukumar ba ta
iya samar musu ba, yadda da kudaden aljihunsu su ka rika wannan aiki baya ga
ajiye harkokinsu domin samarwa masana’antar mafita. Taron da su ka yi da yan
downloading da jami’an tsaro ne kadai hukumar ta dauki nauyi. A karshe ma dutse
a hannun riga su ka rabu da Afakallah ba tare da nuna wata godiya ba ko
tabbatar da abubuwan da su ka kawo domin ci gaban masana’antar. Ya kamata
Afakallah ya farka daga barci ya san cewa sauran shekaru biyu su ka rage masa,
kuma idan ya gama su, cikin masana’antar dai zai dawo, don haka ya rage nasa ya
yi amfani da lokacin da ya rage masa domin tabbatar da cewa ya bar bayan da zai
yi alfahari da ita.
Ita kuwa masana’antar
Kannywood, kamar yadda duk sauran al’amuran hausawa su ke a yau, ta kasance ba
wani abu da za’a hadu ayi aiki tare domin gudu a tsira tare, kowa biyan
gajeruwar bukatar sa ita ce a gabansa. Idan mu na da hankali, a yau ba mu da
wata masana’anta wadda za ta iya samarwa dimbin matasan mu aikin yi da kudaden
shiga kamar Kannywood. Domin kamar yadda na taba fada a wani rubutu na a baya,
a yayin da marubucin fim ya dora bironsa a kan takarda, daga nan ya fara samar da
ayyukan yi da su ka hada da jarumai, masu shiryawa, bada umarni, daukan hoto,
masu tacewa, tsara wajen aiki, masu buga takardu, masu ababen hawa na haya,
masu otal-otal, madinka, yan talla, masu kasuwanci, masu rarraba fim da
tallansa, gidajen rediyoyi da talabijin kai hatta matan aure a gidajensu
wadanda ke dafa abinci akai wurin daukar fim ko bada hayar sutura. A kalla
akwai kimanin sana’o’i 26 da ke da alaka da yin harkar fim. MOPPAN ta gaza
wajen samar da ingantaccen shugabanci a kungiyoyin kwararru (guilds) da ke
karkashinta wanda ta hanyarsu za’a iya samarwa da yan masana’antar tallafi a
karfafa su kuma idan ta kama a ladabtar da su. Yawancin wadannan kungiyoyi
karkashin MOPPAN za ka samu a rarrabe su ke yadda da yawa na da shugabanci guda
biyu masu hamayya da juna. Ita kanta MOPPAN din mu na iya cewa ba tsaye ta ke
dakafufuwanta ba domin ba ta da ingantattun hanyoyin samun kudin shiga yadda
wasu lokatai ko kudin haya ba sa iya biya daga asusun su.
Ginshikin kowacce masana’antar
fim a duniya bayan saka jari ita ce samun ingantacciyar hanyar kyautar karramawa
(Awards) domin ita ke jawo hankalin masu saka jari, samar da ingantattun
fina-finai da kuma tabbatar da gogayya da azama ga duk wanda ke cikin masana’antar
wajen ganin ya inganta abinda ya ke yi. An wayi gari a Kannywood yau babu wata kyautar
karramawa ta azo gani sakamakon guda dayar da ake zaton za ta kai gaci an barta
ta mutu, wadda ke nan kuma a yanzu masu jagorantarta baki ne wadanda, ba abinda
za su samarwa masana’antar ce a gabansu ba sai dai abinda za su samu daga
masana’antar. Ita kanta gwamnati Kano da tana da masu bata shawara da ta ware a
kallah miliyan hamsin duk shekara domin samar da irin wannan karramawa ta
gwamnati, ba don komai ba sai don zai habaka harkar a masana’antar yadda za ta
iya kawowa jihar masu saka jari sannan za ta iya samun kudaden shiga ninkin
abinda su ka saka duk shekara idan abin ya karbu, abinda su Afakallah da yan
uwansa na Kannywood da ke cikin gwamnatin ya kamata a ce tuni sun saidawa gwamnati.
Ya kamata masu sana’a a masana’antar da kungiyoyi har da ita gwamnati, gaba dayanmu mu farka mu gane cewa wannan masana’anta tamkar saniya ce mai jiran tatsa, idan muka tashi tsaye za mu ci moriyar ta, amma idan mun ci gaba da son kai ba tare da la’akari da gina masana’antar ba, hakika za mu wuce mu bar ta, domin ko ka ki ko ka so, masana’antar fim ba abinda zai kauda ta, sai dai watakila idan mun wuce wasu za su zo su tatseta.
Comments
Post a Comment