YADDA ZA'A HANA FARANSA CIN MUTUNCIN ANNABI
Kiyayya ga musulmi, annabi da kur’ani ba sabon abu ne, domin ya samo asali tun farkon zuwan musulunci sakamakon kakkabe bautar gumaka a Makka da murkushe daulolin Farisa da ta Bizantiyawa, wadanda a wannan lokaci su ne daulolin da ke mulkar duniya. Sakamakon haka sai gungu-gungun kabilu su ka rika barkowa su na shiga musulunci abinda ya tsananta kiyayya ga musulmi. Bayan kafuwar musulunci, addinin ya kai kudancin Asia a farkon karni na 8 lokacin da sojojin musulunci karkashin jagorancin Mohammad Bn Kassim su ka isa gabar Sind a shekarar 711. Haka nan a daidai wannan lokacin ne kuma Tariq Bn Ziyad ya isa Gibraltar (wadda ta samo sunanta daga sunansa a larabce wato Jabar al-Tariq) wadda a yanzu ke karkashin kasar Sifaniya da ke turai. A wajajen karni na 14 kuma daular Usmaniyya (Ottoman empire) ta kafa na ta sansanin a turai da wasu sassa na Rasha a yanzu. Sakamakon daruruwan shekaru na hamayya tsakanin addinan musulunci da na kiristanci a turai, ya haifar da yake-yaken crusade wadanda Fadar paparoma ta yi ta haifarwa domin ganin an kakkabe musulunci kwata-kwata daga duk wata kasa ta turai.
A shekarun baya-bayan nan tsanar musulunci ta yi katutu ne a kasashen Turai da na Amurka, wanda bai rasa nasaba da bayanin shahararren marubucin nan Huttington, wanda cikin littafinsa mai suna “Clash of Civilization” ya bayyana cewa kasancewar turawan yamma sun ga bayan tsarin kwaminisanci bayan ture katangar Berlin a shekarar 1989, hankalinsu kacokan ya koma kan yakar musulunci. Masani dan kasar Faransa, Alain Quellin shine wanda ya fara amfani da Kalmar Islamophobia a nazarinsa na samun digirin digirgir a shekarar 1910 inda ya fassara Kalmar da cewa “Wato nuna banbanci da wariya, kyama da kuma dankwafe musulunci yadda ake kallon musulunci da musulmi a matsayin abokan gabar turawan yamma”
A yan shekarun nan ba wata kasa da ta fito karara ta ke nuna kiyayya ga musulunci da musulmi kamar kasar Faransa, duk da cewa ita ce ta fi kowacce kasa a turai yawan musulmi. Maimakon kokarin ganin cewa musulmanta sun zama cikakkun yan kasa, sai su ka dauki damarar tsokana da harzuka musulmi ta hanyar bada damar cin mutunci abubuwan da musulmin su ka dauka da daraja sosa da sunan yancin fadin albarkacin baki. Musulunci shine addinin da ya fi kowanne saurin yaduwa a fadin turai, ba domin turawa na musulunta ba, sai dai sakamakon musulmi na yin hijira kasashen turai kuma sun fi turawa yawan haihuwa. Hatta rikicin Brexit idan aka nutsu za’a iya gane cewa Birtaniya ta yi kokarin ficewa daga tarayyar Turai saboda ganin yadda musulmi ke kwarorowa cikin yankin kuma dokokin kungiyar tarayyar Turai na basu damar zama yan kasa, musamman ganin yadda Angela Merkel bayan guguwar canji da ta faru a kasashen larabawa (Arab Spring) ta bude kofofin Jamus domin karbar yan gudun hijira miliyan guda. Birtaniya ta yi kokarin kaucewa zama cikin hadakar turai kasancewar ita ce kasa ta biyu mafi yawan musulmi. Daga shekarun 2010 zuwa 2016 yawan musulmi ya karu a turai da kimanin kashi 32%, kuma masana kididdigar yawan jama’a a wani bincike na su ya nuna cewa koda ba’a ci gaba da karbar bakin musulmi a turai ba, nan da shekaru 100 zuwa 200 kimanin manyan kasashen turai 13, ciki har da Birtaniya da Faransa, za su wayi gari yawan musulmi ya haura na sauran turawa a kasashen, sakamakon cewa a lokacin da musulmi ke kara haihuwa, turawa rage haihuwa su ke.
Kasar Faransa ta zabi daukar yanayin rura wutar banbanci tsakanin musulmi da turawa ta hanyar cin mutuncin addinin yadda ko kasar Amurka da ake ganin ta kai tsaiko a wajen fadin albarkacin baki, ba ta bari an yada hotunan batanci da jaridar Charlie Hebdo ta yada na manzon Allah a kasarta ba. Wannan tsari na Faransa ya faro tsamari ne a zamanin Sarkozy wanda ya kulla yaki da musulmi ta hanyar zungurar abubuwa da za su harzuka musulmi, misali hana saka hijabi a makarantun Faransa da kuma kare yancin yada hotunan batanci na annabi har ma da saka hannu tare da wasu mutane 300 da su ka yi kiran cewa a yi wa Qur’ani kwaskawarima. Sarkozy ya gama shedancinsa sai ga shi rikicin cin hanci wanda aka zargi kasar Libya na baiwa kanfen dinsa kudade ya jawo faduwarsa a zabe kuma har kotu ta fara tuhumarsa.
Irin wannan hanya da Macron ke kokarin bi ba za ta haifar masa da da mai ido ba, kamar wanda ya gada. Macron na amfani da wannan hanya ne ganin cewa jin ra’ayin yan kasar Faransa ya nuna kaso 78% sun gamsu cewa a karkashin mulkinsa faransa ta ja baya kuma wasu kaso 27% na ganin cewa ba zai iya ceto kasar ba. Wannan ya sa shi farfado da tunzura musulmi yadda zai sami hadin kan yan kasar sa. Bayan an sare kan malamin makarantar nan wanda ya nunawa dalibansa hotunan batanci ga manzo, Macron ya yi wuf ya cafi lamarin domin samun goyon bayan yan kasarsa inda ya ke kare damar nuna hotunan a matsayin yancin fadar albarkacin baki. Sannan ya gaggauta rufe cibiyar da ke nazari da kula yadda ake kyamatar musulunci da musulmi a kasar tare da wasu masallatai. Gwamnatin Faransa a kokarinta na gina tsana ga musulmi ta saka koyar da yancin fadar albarkacin baki a manhajar makarantun yara. A bayyane ya ke ga duk mai hankali cewa yancinka bai baka damar shiga yancin wani ba, kuma duk da wannan ikirari da su ke yi na karya, idan ka duba yadda basa yarda da cin zarafin yahudawa kasan zancen banza ne. Hakika matukar za su ci gaba da wannan rashin adalci da tsanar musulmi ba abinda zai kawo zaman lafiya tsakanin Faransawa da duniyar musulmi.
Inda za ka tabbatar da ikirarin Faransawa na fadar albarkacin baki karya ne kuma kawai fakewa ce da uzzurawa musulmi, bayan shugaban Turkiya Erdogan ya fito ya soki wannan matsaya ta Macron tare da umarnin a kauracewa kayan faransa sai ga shi ya umarci jakadan Faransa ya baro Turkiya. Idan har wannan zai iya saka shi dambarwa da Erdogan mai ya ke tsammani musulmi za su yi idan an ci mutunci annabinsu? Wani jajirtaccen shugaban musulmi shine Imran Khan na Pakistan wanda shi ma ya yi irin wannan umarni. Amma abin takaici shine yan’uwanmu mafi karfin tattalin arziki da alakar cinikayya da Faransa, wato Saudia da UAE sun yi gum ba wanda ya ce kanzil. Kuma wadannan biyun su kadai sun isa su durkusar da Faransa domin a bara kasar UAE ta yi cinikayya ta kimanin Euro Biliyan 279 da Faransa yayin da Saudia ke cinikayya ta makaman da take yaki da Yemen na biliyoyin daloli. Idan Saudi da UAE za su sakawa Faransa takunkumi, wadda kashi 50% na cinikayyar ta da kasashen waje kan makamai ce kuma larabawa ne manyan kawayen cinikinta, hakika da Faransa ta shiga taitayinta.
Abin takaici shine larabawa ba za su iya tsayawa domin kare musulunci ba duk da cewa Allah ya basu makamin, wato karfin tattalin arzikin na mai. Shi bature ba abinda ke gabansa illa arzikin duniya don haka da shi kadai zaka iya juya shi amma kasashen musulmi sun kasa gane damar da Allah ya basu. Lokaci ya yi da musulmi ya kamata su farka su fara amfani da makamin kauracewa duk wata kasa da ta raina musu addininsu. Mu na ganin yadda Yahudawa, wadanda ba su fi cikin cokali ba, amma sun yi amfani da karfin tattalin arzikinsu wajen kaucewa duk irin wannan cin mutunci, ba ma na addininsu ba har al’adunsu da tarihinsu. Yanzu a kasashen turai ba ka isa ka ce Hitler bai azabtar da su ba. A makon nan mun ga yadda jam’iyyar Labor ta Birtaniya ta dakatar da Jeremy Corbin, wanda ya yi mata takarar shugaban kasa kwanan nan, akan cewa lokacin shugabancinsa ya yi sakwa-sakwa da yancin yahudawa.
Faransa ta fi kowacce kasar turai mugun hali idan ka yi la’akari da yadda ta yi mulkin mallakar ta, wanda har yanzu kasashen renon Faransa ba su da banbanci da bayin Faransa domin hatta kudin da su ke tu’ammali da shi daga bankin Faransa ake bugawa a basu (saifa). Yaren da Faransa ta sani kawai shine na abin duniya, kuma Allah ya horewa kasashen musulmi arziki, don haka mu tashi mu fara amfani da wannan makami. A duk lokacin da wani ko wata kasa ta ci mutuncinmu ko addininmu to da zarar an busa usur kowa ya kauracewa kayansu. Wallahi wannan ce hanya kadai da za ta sa a daina raina mu da addinimu da manzon mu. Don haka na barku da kayan Faransa da ya kamata mu kauracewa: Orange (telecom) Total (oil) Chanel (Luxury), Garnier (care), Lious Vutton (luxury), Peugeot (automobile), BNP Paribas, Hennessy, Renault, BIC (the biro), Societe Generale (Bank), CANAL+, Airbus, Lacoste, Givenchy, Vichy, ELF, Michellin, Citreon, Dior da duk wani kaya da kuka ci karo da shi.
Comments
Post a Comment