MALAMAI SUN TAIMAKA WAJEN RUSA AREWA
Malaman mu, walau na kirita ko
musulmi, na da hannu wajen rushewar yankin arewa. Arewacin Najeriya tun daga
samun yancin kai har zuwa farkon mulkin sojoji, duk da banbance-banbancen
addini da kabila, ana zaune lafiya kuma an fara samun habaka. A koyarwa ta
manyan addinan mu guda biyu, Malamai su ne wadanda ya kamata su zama masu
kariya ga tarbiyya da zamantakewa. Kuma babban aikinsu shi ne na kare gaskiya
daga duk inda ta fito, amma sai a ka wayi gari sun kauracewa gaskiya ballantana
ma su kare ta. Bari na bada wani gajeren misali. A lokacin mulkin Babangida,
matarsa ta yi kokarin kafa hukumar Better life domin wayar da kai da samar da
hanyoyin karfafa tattalin arziki. A irin tarukan da aka rika yi a jihohi na
kaddamar da wannan shiri, a wata Jiha an zo wajen taron inda a ka gayyato wani
babban malami da zai yi addu’a da kuma dan gajeren bayani. Yayin da aka kira
wannan malami ya isa wajen lasifika, sai ya juya ya tambayi mutumin da ya gayyato
shi “Shin ku na son a soki wannan lamari ne ko kuwa kun a so ne a yabe shi?” Irin
wannan mu’amala tsakanin malamai da al’umma ita ta zama ruwan dare a ko’ina
cikin yankin nan.
Irin wannan zaizayewar da’a da son
duniya a tsawon shekarun da su ka gabata shine ya baiwa yan siyasa damar sanya
malamai cikin aljihunsu yadda ba su da wani katabus sai abinda yan siyasa su ka
karkata su a kai. Malamanmu baya ga daura aure da yan siyasa sai kuma su ka yi
saki ga zumunci na zamantakewa a tsakanin addinai wanda ya garkame duk wata
hanya ta ci gaban yankin. Shugaba Babangida, sakamakon gazawarsa na ganin an
yankewa Zamani Lekwot hukuncin kisa da wata kotu ta yi masa sakamakon samunsa
da lailfin hura wutar rikicin Zangon Kataf a shekarar 1987, shine ya dinke mu a
halin da muka sami kan mu na kashe-kashe a dalilai na addini da kabilanci
tsakanin manyan addinan guda biyu. Da an aiwatar da wannan hukunci na tabbatar
da ‘yan baya sun ji tsoron amfani da wannan hanya wajen lalata arewa.
Kungiyoyin CAN da na Jama’atul Nasril Islam sun ja daga kowa baya iya kallon
gaskiya sai idan shi ta shafa kuma hakan ya kara ruruta wutar kabilanci da
banbancin addini wanda ya yi mana tarnaki kuma ya hana mu ci gaba a Arewa.
Ana nan kuma sai rikicin Boko Haram
ya bullo yadda a lokacin Jonathan malaman addinin musulunci su ka bazama wajen
yin huduba a masallatan jummu’a ana ta tsinewa gwamnatinsa ba tare da wata
kakkausar su ka ga su yan Boko Haram din da akidojinsu ba. Zaben 2015 ya
kasance a Arewa tamkar zabe ne tsakanin kirista da musulmi maimakon PDP da APC.
Haka nan wadannan malamai su ne a yau su ke kare gwamnatin Buhari da hana a
soke ta da sunan cewa hakan ya sabawa addini duk da cewa masifun da ake
fuskanta a yau sun zarce na lokacin Jonathan wanda ya ke a kan Boko Haram ne
kawai, sun hado da ta’addanci, dabanci da sace-sacen jama’a domin neman kudin
fansa.
A yau Arewa na cikin bala’o’i da ba
mu taba ganin irinsu ba kuma a daidai lokacin da Dan Arewa ke mulki kuma wasu
kaso na manyan Malaman Arewa ke kusa da gwamnati. Idan ka cire jihar Kano da
Jigawa, ilaharin Arewacin Najeriya a cikin mummunar matsalar rashin tsaro ya
ke. Ita kanta Kano wasu na ganin cewa dalilin da ake zaune lafiya saboda ta
zama wata matattara ta duk wasu miyagu da ke aiwatar da munanan abubuwa a
yankin, nan su ke zuwa su sami mafaka kasancewar garin ya zama kamar rariya
yadda kowane kare da doki zai iya shiga garin ya kama haya ba wani cikakken
bincike musamman a sabbin unguwanni da ke gefen garin. Wannan ya sa an kama wasu
yan ta’adda da dama a garin yayin da wasu su ka buya a ciki na tsawon watanni ba
tare da an sani ba.
Wannan dalili ya sa na yi wani yunkuri
a makon da ya gabata na kokarin hado wakilan duk manyan kungiyoyinmu a Kano
(KCCI, Kano leads, NDF, ADSI) da kuma wasu manyan malamai domin a zauna a duba
wata shawara da na ke tunani. Na tuntubi Alh. Bashir Tofa domin ya jagoranci
shirin, kasancewarsa a kullum a shirye ya ke da daukar ragamar duk wani abu na
ci gaban Kano. Haka nan na gayyaci Ashiru Nasdura, shugaban hadaddun kungiyoyin
Arewa. A cikin manyan malaman da na gayyata, wadanda kowanne ya na jagorancin
wani babban masallacin Jummu’a a Kano duk sun amsa min za su halarta bayan na
gaya musu abinda na ke so mu fuskanta. Amma cikin malaman nan guda daya ne ya
sami halarta shi ma kuma sai a karshen taron.
Abinda na so muyi shine kasancewar
yan siyasa, masarauta da yan boko basu da wata kima a fuskar al’umma amma su
malamai duk da suma kimar ta su ta ragu sosai amma dai su kadai su ka rage
cikin al’umma wadanda ke da hanyar kaiwa kai tsaye ga al’umma kuma ana
sauraronsu ta hanyar masallatai musamman na jummu’a. Idan da malaman za su ja
ragamar kafa kwamitoci a kowanne massallacin jummu’a a jawo mutane da ke wannan
yanki kama daga kwararru na fannoni, yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati da
sauransu yadda kowacce unguwa ta na da manya wadanda za su rika tattauna
matsalolinta da samar da hanyoyin warware su. Idan har zamu karfafa irin wannan
kwamitoci a ko’ina za mu iya dawo da tsarin tsaro, farfado da harkar ilimi,
kasuwanci har ma da siyasa. Duk al’ummar da ta zabi zama kara-zube dole ta sami
kanta a irin wannan hali da mu ke ciki kuma idan ba mu ajiye son kai da rungumar
sadarkarwa ba, to hakika babu yadda za’a yi mu sami saukin matsalolin da mu ke
ciki saidai kullum su ta’azzara kamar yadda mu ke gani a yanzu. Idan malamai ba
za su iya haduwa a ceto al’umma ba, wanene zai yi? Kuma su malaman nan
kasancewar sun yi watsi da fadar gaskiya sun koma kwadayi ga mahukunta shine asalin
dalilin da ya jefa mu halin da mu ke ciki. Duk yunkurin nawa ya tashi a banza
saboda malaman ba su bada hadin kai ba, kuma a cikinsu dama akwai wanda ya fito
baro-baro ya ce min duk da tunanin mai kyau ne, zai wahalar aiwatarwa saboda
idan ba gwamnati ce ta kira su ba, ba za su iya sauraren daidaikun mutane irin
mu ba.
Kullum Kiristoci da mu musulmi muna
zagin Yahudawa amma kuma a zahirance sun fi mu sanin abinda su ke yi, sakamakon
cewa duk wani abu da ya shafesu su na hade kansu waje guda. A yau, Yahudawa ke
mulkin duniya sakamakon sun assasa ilimi da son juna da taimakon junansu. Tun
bayan yakin Yahudawa da Larabawa na shekarar 1973, sun lashi takobin ba za su
sake zama yadda wani al’amari zai mamaye su ba. Domin a shekarar 1948 Hitler ya
yi musu bazata inda ya kama miliyoyinsu ya karkashe sannan Larabawa sun far
musu da yaki a 1973 katsam duk da a karshe dai su ne su ka sami nasara kan
larabawan. Tun daga wancan lokaci su ka ware wasu fitattun Yahudawa da su ka yi
wa lakabi da dattawa goma (goma ita ce adadin abubuwan da Annabi Musa ya fara
karbowa na wahayi a wajen Ubangiji). Wadannan dattawa goma su na bincike da
nazari mai zurfi akan al’amura na yau da kullum domin hasashen ta ina za’a iya
far musu. Duk wani abu da su ka yi hasashen zai iya zuwa ya far musu, kafin fa
ya zo, za su samo wata hanya da za su lalata wannan abu kafin ma ya yi tasiri.
Sannan Yahudawa sun assasa Zakka a tsakaninsu yadda Attaura ta umarce su, kuma
a yanzu a doron duniya babu masu fitar da zakka tamkar su. Wannan ya sa da wahala
ka ga Bayahude talaka fitik. Shin zakkar nan ba Allah mu hade mana ita ya yi da
imani ba? Wa ke yin zakkar yadda Allah ya ce? Kashi saba’in na matsalolin
musulmi na talauci ne kuma da za mu assasa zakka a tsakanin mu hakika da mun kawar
da wannan talauci. Wanene da hakkin assasa zakka a idanuwan musulmi fiye da
malamai, amma sun fi maida hankalinsu akan abubuwa da Allah ma ba zai titsiye
su a kansa ba amma sun bar ginshikin addini ba ruwansu da shi. Idan ka ga
malaman mu na tada jijiyar wuya to abubuwa ne da ba su zama wajibi a kan
kowanne musulmi ba, ko kuma rigima ce ta bangaranci. Malamai su sani cewa Allah
ya dora musu hakkin al’umma domin kamar yadda ake cewa su ne magada annabawa, to
amma shin halayyar su a yanzu ta nuna cewa sun cancanci wannan lakabi a
arewacin Najeriya a yau?
Allah ya sa Su gane.
ReplyDeleteAli Allah Ya biya ka, wannan rubutu ya yi ma'ana. Allah Ya sa sakon ya je ga wadanda aka yi dominsu. Ya kuma basu ikon fahimta.
ReplyDelete