BUHARI ZAI KASHE MU DA BASHI

A watan October na shekarar 2005, Nijeriya da kungiyar Paris Club mai bada basuka ga kasashe sun sanar da yarjejiniyar yafewa Najeriya bashin da ya kai dala biliyan $18 tare da rage kudaden ruwa da ya kai dala biliyan $30 billion. An kammala wannan yarjejeniya bayan Najeriya ta gama biyan karshe na bashinta wanda ya sa aka yafe ragowar a ranar 21 ga watan Afrilu na 2006. Wannan lokaci na da matukar mahimmanci ga Najeriya kuma da a ce mahukunta daga wancan lokacin zuwa yanzu sun yi abinda ya kamata, da tuni kasar ta shiga jerin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki. Bayan yafe wannan bashi, bashin kasar ya zama dala biliyan $3.5 kacal, amma bayan shekaru 15 sai ga shi bashin ya sake habaka inda a wannan shekara ta 2020 kamar yadda hukumar da ke kula da basukan kasar (Debt Management office DMO) ta sanar da cewa bashin ya kai Naira Tiriliyan 31.01 (wato dala biliyan $85.9). Matsayin yawan bashi idan an kwatanta da karfin arzikin kasa ya karu zuwa kaso 28%, sama da yadda ya ke a wasu matalautan kasashen Afirka kudu da Hamada. A tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019, gwamnatin Najeriya ta kashe kimanin Naira Tiriliyan 34.83 trillion (wato dala biliyan $88.3), inda kaso 73.1% a ka kashe su wajen ayyukan yau da kullum, sannan kudaden ayyuka kuma su ka sami kaso 19.2 yayinda aka biya kaso 7.8% zuwa basuka. Karbar bashi ba kai ba gindi da wannan gwamnati ke yi ya karu da kaso 34.6% a zuwa watan Yuni na 2020. Takardun lamunin kasar da ake kira Euro Bond, zai cika a watan Janairu na 2021, abinda masana ke ganin zai iya kawowa kasar tsaikon samun wasu basukan

La’akari da wadannan bayanai ya nuna cewa kaso 19% ne kacal na wadannan makudan basuka da aka ciwo su ka tafi kan ayyukan raya kasa. Kididdigar bankin duniya ta nuna cewa Najeriya na da gibin ayyukan raya kasa wanda ko da za’a rika saka dala biliyan $100 duk shekara, sai an yi shekaru da dama kafin a sami cike wannan gibi. Ita kanta ministan kudi ta nuna cewa kudaden da ake sakawa a fannin raya kasa kashi 30% ne wanda a ka’idar kasashen duniya domin cimma burika na karni ya kamata  a ce ya kai kashi 70%. Sannan wannan gwamnati ta mai d a hankali kacokan wajen saka kudaden raya kasa wajen gina tituna da hanyoyin jirgin kasa inda aka yi shakulatin bangaro da harkokin ilimi da na masana’antu.

Ministan ayyuka, Babtunde Fashola, a karshen shekarar da ta gabata ya shaidawa kwamitin ayyuka na majalisar wakilai cewa ma’aikatarsa na aiki a kan hanyoyi guda 524 a sassan kasar guda shida, amma ba za ka iya nuna wani babban aiki kwaya daya da aka kammala cikin wadannan shekaru biyar ba. Hanyar Lagos-Ibadan wadda aka ba da kwangilar ta a kan kudi Naira biliyan 167 mai tsawon kilomita 127 har yanzu ba ta kammalu ba inda ministan ke cewa sai a shekarar 2022 za’a iya gama aikinta. Haka ita ma hanyar da ta taso daga Abuja zuwa Kano wadda aka bada kwangilar ta a kan Naira biliyan 155 ga kamfanin Julius Berger wadda aka ce a satuka 36 za’a kamala aikin, yanzu bayan watanni 28 da fara aikinta, Ministan ya ce sai an kai shekarar 2025 kafin ta kammalu. Wasu yan majalisar wakilai sun nuna shakku lokacin da aka bada aikin inda su ke ganin cewa an yi zure a farashin yin kowacce kilomita daya akan Naira miliyan 450. Kuma ko kun san cewa aikin Gadar Niger ta biyu da aka bayar kan kudi Naira biliyan 336 zai iya gina hanyoyin Lagos-Ibadan da Abuja-Kano? Tsawon wannan gadar kilomita 1.6 sai titin da zai hade hanyoyi da gadar wanda bai wuce kilomita 11 ba. Wato kusan kowacce kilomita idan da tsawon kilomita za’a kwatanta aiki zai lakume naira biliyan 28. Shi kansa wannan aiki minister ya ce sai a shekarar 2022 shi ma zai kammala.

Gaskiya ne cewa babu wata gwamnati da za ta rayu babu bashi amma matsalar ita ce yin amfani da basuka wajen kyautata rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa, abinda ya gagare mu a Najeriya. Duk basukan da kasar ta ci a wannan gwamnati ba wanda ya zamar mana alakakai irin wanda Bankin duniya ya cusa mana a daidai lokacin da ake tsaka da kullen Covid. Bankin da kansa ya nemi Najeriya a watan Fabrairu na wannan shekara su karbi wannan bashi sakamakon matsalar Covid. Masana sun nuna cewa wannan bashi ya zo da tarnaki irin yadda bankin duniya ya saba domin tursasawa kasashe bin wasu ka’idoji kama daga cire tallafi, daidaita canjin kudin kasa da saka haraji. Duk da cewa fa shi wannan bashi ana son bada shi domin kawo sauki ga matsalar da kasashe su ka shiga sakamakon corona. Wani masanin tattalin arziki, Feyi Fawehinmi, ya yi mamakin dalilin da bankin duniya zai matsa wajen saka sharuda a bashi na Covid inda ya ke cewa bankin duniyar bai “Tambayi abubuwa irinsu cibiyoyin killace masu cutar covid nawa mu ka gina ba? Wane irin shiri mu ka yi don dakile yaduwar cutar da kuma samar da kayan tallafi domin taimakawa talakawa matalauta?”

A bayyane ya ke abubuwan da su ka faru a watanni shida da su ka gabata shaida ce cewa hakika gwamnatin kasar ta aminta, dari bisa dari, da sharuddan da Bankin Duniya ya gindaya mata ganin yadda cikin gaggawa gwamnatin Buharin ta cire tallafin mai sannan su ka dauke hankalin jama’a wajen kara kudin mai sannu a hankali har zuwa Naira 173. An fara da yi wa mutane wayo a watan Maris inda sai gwamnati ta sanar da rage kudin mai daga Naira 145 zuwa Naira 125. A karshen watan mayu sai aka sake ragewa zuwa 123 sannan sai a karshen watan Mayu aka sake bada sanarwar an tsaida farashin daga Naira 121 zuwa 123 duk lita. Ana gama wannan yaudara sai kuma aka koma Karin kudin man ba kai ba gindi inda ya koma 143, 151 zuwa yanzu ya ke tsakanin 165 zuwa 173. An cimma burin Karin kudin mai sannu a hankali ba tare da la’akari shi kansa bashin an karbo don kawo sauki ga yan kasa ba, amma ya koma ga uzzura musu. Mun ji yadda Ministan kudi ke maganar sake kara kudin harajin VAT, wanda duk suna cikin sharuddan. Wannan matsi da yan kasa su ka shiga, na cikin abinda ya tunzura matasa su ka fake da zanga zangar Endsar su ka yi ta ta’addanci a fadin kasar. Ya kamata mahukunta su fahimci cewa dole su kula da dimbin matasa da kullum ke karuwa amma ba su da ayyukan yi, don haka wajibi su rage bushasharsu da kudaden gwamnati domin samar da ayyukan yi. Tarzomar Endsar ya kamata ta zama wata kararrawa a gane cewa akwai hadari idan aka ci gaba da zama yadda ake. A kuma fahimci cewa cikin kudaden da ake samu a kasar idan ko da daya bisa hudu aka karkata wajen masana’antu da samarwa matasa basuka da tallafi, zuwa wani lokaci za’a habaka karfin tattalin arziki wanda zai sa gwamnati na iya dogaro da harajin cikin gida, musamman idan mu ka yi la’akari da yadda wannan gwamnati ta samar da hanyoyi masu inganci na karbar haraji a bayyane ba kumbiya kumbiya. Gwamnati na da kyawawan shirye-shirye irinsu NIRSAL wadanda idan aka saka kudaden da ya kamata kuma aka bude abin a fili yadda duk wanda ya cancanta zai iya samu, cikin lokaci kankane za’a ga habakar tattalin arziki. Kananan sana’o’i sune ginshikin duk wani tattalin arziki don haka dole a habaka su kuma musamman akwai miliyoyin matasa wadanda dan jari kalilan su ke nema su tsaya da kafafuwansu. Tarzomar Endsar ya kamata ta bude idanuwanmu mu gane cewa zaman lafiyar kasar shine kulawa da matasa, watsi da su kuma babban hadari ne ga kowa da kowa “ Idan kunne ya ji, jiki ya tsira”

 

 

           

 

Comments

Popular posts from this blog

MALAMAI SUN TAIMAKA WAJEN RUSA AREWA

JINNS: SPIRITUAL FANTASY OR SCIENTIFIC POSSIBILITY?

THE NORTHERN WAHALA!