BUHARI ZAI KASHE MU DA BASHI
A watan October na shekarar 2005, Nijeriya da kungiyar Paris Club mai bada basuka ga kasashe sun sanar da yarjejiniyar yafewa Najeriya bashin da ya kai dala biliyan $18 tare da rage kudaden ruwa da ya kai dala biliyan $30 billion. An kammala wannan yarjejeniya bayan Najeriya ta gama biyan karshe na bashinta wanda ya sa aka yafe ragowar a ranar 21 ga watan Afrilu na 2006. Wannan lokaci na da matukar mahimmanci ga Najeriya kuma da a ce mahukunta daga wancan lokacin zuwa yanzu sun yi abinda ya kamata, da tuni kasar ta shiga jerin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki . Bayan yafe wannan bashi, bashin kasar ya zama dala biliyan $3.5 kacal, amma bayan shekaru 15 sai ga shi bashin ya sake habaka inda a wannan shekara ta 2020 kamar yadda hukumar da ke kula da basukan kasar (Debt Management office DMO) ta sanar da cewa bashin ya kai Naira Tiriliyan 31.01 (wato dala biliyan $85.9). Matsayin yawan bashi idan an kwatanta da karfin arzikin kasa ya karu zuwa kaso 28%, sama da yadda ya ke a...